Matsakaicin saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai 9.8% cikin shekaru 35 da suka gabata
A yau Laraba 6 ga wata, hukumar kididdigar kasar Sin ta bayar da wani rahoto a kan shafinta na intanet, inda ta nuna cewa, bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufofin yin gyare-gyare da bude kofarta ga kasashen duniya yau shekaru 35 da suka gabata, tattalin arzikinta ya samu ci gaba sosai, a cikin shekaru 35, wato tsakanin shekarar 1979 da 2012 da suka gabata, matsakaicin saurin bunkasuwar tattalin arzikinta ya kai kashi 9.8 cikin kashi dari a kowace shekara, amma matsakaicin saurin ci gaban tattalin arziki da sauran kasashen duniya suka samu a cikin wadannan shekarun da suka wuce kashi 2.8 cikin kashi dari ne kawai.
Sannan wannan rahoto ya nuna cewa, a shekarar 1978, matsakaicin yawan kudin shiga da kowane Basine ya samu dalar Amurka 190 ne kawai, amma a shekarar 2012, wannan adadi ya kai dalar Amurka 5680. (Sanusi Chen)