in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS ta yi nazari kan ayyukan bunkasa tattalin arziki na shekarar 2014
2013-12-03 20:16:00 cri
Hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS ta gudanar da wani taro a yau Talata 3 ga wata, inda aka yi nazari kan ayyukan bunkasa tattalin arziki na shekarar 2014. Babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping ne ya shugabanci wannan taro.

A gun taron, an nuna cewa, kamata ya yi a ci gaba da aiwatar da ayyuka yadda ya kamata, da yin kwaskwarima a dukkan fannoni yayin da ake bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da kara inganta tsarin bada hidima ga jama'a, ta haka ne jama'ar kasar za su samu moriya daga nasarorin da aka samu bayan da aka yi kwaskwarima da raya kasa, kuma za a sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki da zaman lafiya a cikin al'ummar kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China