A cikin bayanin nasa, Mr. Spence ya bayyana cewa, kasar Sin ta fahimci barazana, da kalubale da take fuskanta wajen canja salon raya tattalin arziki. Don haka gwamnatin kasar ta amince da rage saurin bunkasuwar tattalin arziki, wanda hakan ya kasance mataki da ke kunshe da tarin hikima.
Har ila yau, sharhin ya bayyana cewa, aikin yin kwaskwarima game da albashi, na da muhimmanci ga kasar Sin. Ya ce kasar Sin ta kokarta don kara albashin jama'a, da nufin kara yawan bukatun sayayya. Haka kuma, aikin yin kwaskwarima game da tsarin hada-hadar kudi, zai yi tasiri wajen tabbatar wannan sauyi.(Bako)