Haka kuma, ma'aunin tattalin arzikin manyan kasashen G7, wato kasashen Amurka, da Birtaniya, da Jamus, da Faransa, da Canada, da Italy, da Japan, shi ma ya samu karuwa har tsahon watanni 6 a jere.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, saurin karuwar tattalin arzikin kasashen Asiya guda 5, ciki har da kasashen Sin, da India, da Koriya ta Kudu, da Japan da Indonesiya, ya samu farfadowa har i zuwa mataki na matsaikacin saurin karuwar tattalin arziki.(Bako)