A wannan rana, Zhu Guangyao ya fadi hakan ne, a gun taron manema labaru da ma'aikatar harkokin waje ta shirya game da gudummawar da tattalin arzikin Sin ya bayar wajen sa kaimi ga samun karuwar tattalin arzikin duniya. Ya bayyana cewa, bisa hasashen tattalin arzikin duniya da asusun ba da lamuni na duniya ya bayar, an ce, a shekarar 2013, yawan karuwar tattalin arzikin duniya zai kai kashi 3.1 cikin 100, kuma idan tattalin arzikin kasar Sin ya cimma burin samun karuwa da yawanta ya kai kashi 7.5 cikin 100, ke nan, yawan gudummawar da tattalin arzikin Sin ta bayar wajen sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya zai kai kashi 27.76 cikin 100, kuma yana mai cewa, ba ma kawai tattalin arziki ya samu karuwa sosai, har ma da ingancinsa.(Bako)