Kakakin hukumar kididdiga ta kasar Sin Sheng Laiyun ya bayyana cewa, idan aka cimma burin aiwatar da manufofin da gwamnatin Sin ta tsara, za a gudanar da aikin raya tattalin arziki na karshen rabin shekarar bana yadda ya kamata, don cimma burin samun bunkasuwa kamar yadda aka tsara. Duk da cewa, yawan alkaluman tattalin arziki da aka samu a bana bai yi kyau sosai ba kamar na baya, amma gwamnatin Sin na da imani sosai game da cimma burin samun karuwar tattalin arziki da yawansa zai kai kashi 7.5 cikin 100. (Bako)