in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron dandalin tattaunawar bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba a Beijing
2013-08-26 17:02:29 cri
Kwanan baya, kungiyar kula da bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba ta duniya ta shirya taron dandalin tattaunawar bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba a birnin Beijing, babban birnin kaar Sin.

Taron ya mai da hankali a kan nauyin da ke bisa wuyan kamfanoni da masana'antu da samun dauwamammen cigaban tattalin arziki da bunkasa tattalin arzikin shiyya shiyya ba tare da gurbata muhalli ba, da gyaran tsarin masana'antu da hadin gwiwar kasa da kasa kan fasahar kiyaye muhalli da makomar tattalin arzikin duniya ba tare da gurbata muhalli ba da sauransu, a wani kokari na tattauna matakan da za a dauka don bunkasa tattalin arziki ba tare da kiyaye muhalli ba, tare da samar da shawarwari ga kasa da kasa ta bangaren bunkasa tattalin arzikinsu. Ban da haka, taron ya kuma samar da jerin sunayen masana'antun kasar Sin 100 da suke kan gaba ta fuskar samun yalwatuwa ba tare da gurbata muhalli ba.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China