Masanin tattalin arziki na kafar yada labaru ta Bloomberg ya nuna cewa, bayan Sin ta nuna sanyin jiki wajen saurin bunkasuwar tattalin arziki a farkon watanni shida da suka gabata, yanzu kasar tana samun bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata kuma cikin dorewa, an yi kiyasin cewa, Sin za ta cimma burinta na samun karuwar GDP na kashi 7.5 bisa dari a wannan shekara.
Kamfanin Bloomberg ya tattara ra'ayoyin masu bincike 52 daga ranar 15 zuwa 20 ga watan Augusta, inda binciken ya nuna cewa, Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arziki a shekarar 2014. An ce, bunkasuwar tattalin arzikin Amurka da farfadowar tattalin arzikin nahiyar Turai na taimakawa kasar Sin wajen fitar da kayayyakinta zuwa wadannan kasashe. Kuma babban mai nazari ta fuskar tattalin arzikin kasar Sin na bankin RBS na Scotland Mr Louis Kuijs ya furta cewa, a halin yanzu da duniya ke neman daga saurinta na farfadowar tattalin arziki, babban ginshikin bunaksuwar tattalin arziki shi ne sha'anin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, wanda zai samu bunkasuwa a karshen wannan shekara. (Amina)