Babban satakaren kungiyar tarayyar kasashen Larabawa wato AL Nabil al-Arabi ya bayyana a ran 20 ga wata cewa, ana kyautata zaton cewa, za a shirya taron Geneva karo na biyu kan batun kasar Sham daga ranar 23 zuwa 24 ga watan Nuwamba na bana.
Nabil al-Arabi ya yi wannan bayani ne a ganawar sa da Lakhdar Brahimi,manzon musamman na MDD da AL mai kula da rikicin Sham a cibiyar kungiyar ta AL da ke birnin Alkahira.
A ganawar , sun tattauna kan halin baya-bayan da ake ciki a Sham, da kuma ayyukan da ake gudanarwa wajen warware rikicin siyasa a kasar Sham, domin share fage ga taron Geneva karo na biyu.
Shi kuma Lakhdar Brahimi ya bayanin cewa, 'yan adawa daga kasar Sham za su halarci wannan taron Geneva.(Danladi)