A cewar John Kerry, masu binciken MDD sun riga sun tabbatar da cewa an kai farmaki da makamai masu guba a kasar Sham, lamarin da a ganin kasar Amurka, gwamnatin kasar Sham ce za ta dau alhaki. Don haka, Kerry ya yi kira ga kwamitin sulhu da ya samar da wani tsari mai karfi don tabbatar da ganin an cimma burin kau da makamai masu guba daga kasar, kuma cikin sauri.
A wannan rana kuma, shugaban kasar Rashan Vladimir Putin, ya ce yanzu haka ya kamata a tabbatar da cewa wane bangare ne na kasar Sham ya kai farmaki da makamai masu guba, sa'an nan kwamitin sulhu zai duba hukuncin da za a yanke masa.
Haka zalika, kamfanin dillancin labaran kasar Sham ya ba da labari a ranar 19 ga wata cewa, shugaban kasar Bashar Assad ya ce kasarsa za ta yi kokarin lalata makamanta masu guba bisa kudurin MDD, sai da za a kashe dalar Amurka biliyan 1 don gudanar da aikin, gami da kwashe shekara guda.(Bello Wang)