Shugaban kasar Sham Bashar Al-asaad ya bayyana a wani shirin gidan talibijin din kasar a daren jiya Litinin 21 ga wata cewa, ya zuwa yanzu, babu alamar dake nuna cewa za a samu wani ci gaba a taro karo na biyu na kasa da kasa a Geneva.
Yayin ganawarsa da kafar yada labaran, Bashar Al-assad ya ce, wani muhimmin abu dake shi ne matsayin da jami'iyyar mahalartan taron suka dauka, ko suna wakiltar jama'ar Sham ko kasashen da suka kawo su nan. Ban da haka, Shugaba Bashar ya zargi wasu jam'iyyu wadanda suka yi shelar mamaye filayen kasar har na kashi 70 bisa dari, a yayin da 'yayansu ke boye a kasashen waje, domin suna tsoron dawowa kasar.
Ban da haka, Bashar ya jaddada niyyar da kasar ke dauka na warware rikicin kasar cikin gida, sannan ya nanata cewa, idan an cimma nasarar kiran wannan taron, gwamnatin kasar Sham za ta tura wakilinta ba tare da gindaya ko wane sharadi ba, kuma babu sauran mataki da za ta dauka. (Amina)