in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren harkokin waje na kasar Amurka ya zargi gwamnatin kasar Sham na kwace shaidun yin amfani da makamai masu guba
2013-08-27 15:05:47 cri

Sakataren harkokin waje na kasar Amurka John Kerry ya fitar da sanarwa a ran litinin 26 ga wata, inda ya zargi matakin da gwamnatin kasar Sham ta dauka na kwace shaidun kai harin makamai masu guba, abin da ya ce ba za a lamunta ko kadan ba, kuma ya kamata, kasar ta amsa laifinta.

Ban da haka, Kerry kuma ya yi zargin cewa, gwamnatin kasar ba ta amince da bincike da MDD za ta yi a wurin ba, sannan ta ci gaba da kai harin igwa a wurin. Gwamnatin kasar Sham za ta iya tabbatar da cewa ba ruwanta cikin lamarin, muddin ta hada gwiwa da MDD.

Dadin dadawa, Kerry ya ce, shugaban kasar Amurka Barack Obama yana tattaunawa kan batun kasar Sham tare da majalisar dokokin Amurka da dai sauran kasashen kawayenta, kuma za a gabatar da matakin da gwamnatin kasar za ta dauka kan al'amarin.

Game da jawabin da Kerry ya bayar, kafofin yada labarai na kasar ciki hadda Wall Street Journal sun nuna cewa, abin ya kasance wata alama ce dake nuna cewa, Obama zai kai hari kan kasar Sham.

Amma, bisa matsayin da Obama ya nuna a cikin hirarsa da wasu manema labari a baya, yana son daukar matakin soja bayan samun izni daga kwamitin sulhu na MDD. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China