in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba zan yi shawarwari da 'yan adawa ba, in ji shugaban kasar Sham
2013-09-30 14:17:33 cri

Shugaban kasar Sham Bashar Al-Assad ya ce ko alama ba shi da wani shiri na tattaunawa da 'yan adawar kasar, muddin suna ci gaba da rike makamai.

Shugaba Assad ya bayyana hakan ne yayin wata zantawarsa da wani wakilin gidan telibijin na kasar Italiya a kwanan baya, yana mai cewa, a hakika dukkan 'yan adawar kasar, 'yan ta'adda ne, don haka gwamnatinsa ba za ta yi shawarwari da su ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Sham ya ruwaito Bashar din na cewa, ayyukan da wadannan kungiyoyin adawa masu dauke da makamai suka yi, sun hada da lalata kayayyakin hukuma, da kisan gilla da sauransu. Don haka duk wata kasa a duniya tabbas za ta dauke su 'yan ta'adda.

Yayin wannan zantawa tasa da manema labaru, Bashar ya nanata aniyyar gwamnatinsa ta bin daftarin kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya zartas a kwanan baya, wanda ya ce ya dace da moriyar kasar Sham gaba daya.

A cewarsa kasar Sham za ta nace ga bin wannan kuduri, ba tare da jingina ko wane sharadi ba.

A hannu guda kuma, jigo a kungiyar NCBDC ta 'yan adawa mafi girma a kasar Safwan Akkasheh, ya shaidawa manema labaru cewa, kasashen duniya sun riga sun cimma matsaya guda, kan batun daukar matakin kiran wani taron kasa da kasa, domin samo hanyar warware batun kasar ta Sham a tsakiyar watan Nuwamba, a birnin Geneva na kasar Switzerland. Ya ce ya kamata dukkan jam'iyyun kasar su halarci taron, kuma su ba da gudummawar cimma nasarar taron yadda ya kamata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China