Kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taro cikin gaggawa a wannan rana domin tattauna kan batun, kuma babban sakatare Ban Ki-Moon ya ba da sanarwa ta bakin kakakinsa a ran 22 ga wata, inda ya nanata wajibacin nazari kan wannan batu cikin sauri, kuma ya ce, ya tura jami'an MDD zuwa kasar Sham.
Kakakiyar ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka Madam Jen Psaki ta bayyana a ran 22 ga wata cewa, gwamnatin kasar tana hadin gwiwa da kawayenta da wasu kasashen yankin gabas ta tsakiya domin dudduba kan lamarin tun da wuri. Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Rasha Alexander Lukashevich ya bayyana a ran 22 ga wata cewa, matsayin da kasar za ta dauka kan wannan lamari ya dogaro da binciken da MDD take yi. (Amina)