in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sham ta shiga cikin yarjejeniyar haramta makamai masu guba a hukunce
2013-10-15 10:49:33 cri

Kungiyar haramta makamai masu guba ta gabatar da wata sanarwa a ran 14 ga wata cewa, daga wannan rana yarjejeniyar haramta makamai masu guba ta fara aiki kan kasar Sham, wato ke nan kasar Sham ta zama mamba ta 190 ta Kungiyar.

Kungiyar ta bayyana cewa, kasar Sham ta gabatar da takardun neman zama mamban kungiyar a ran 14 ga watan jiya. A gun taron hukumar zartarwa karo na 74 na kungiyar da aka shirya daga ranar 8 zuwa 11 ga wannan wata da muke ciki, an dudduba takardun da Sham ta gabatar. Bisa abubuwa da aka tanada cikin yarjejeniyar, an ce, yarjejeniyar haramta makamai masu guba za ta fara aiki kan Sham daga ranar 14 ga watan Oktoba a hukunce.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China