Taron wanda ya maida hankali ga tattauna hanyoyin warware rikicin kasar ta Sham, da batutuwan da suka shafi taro na biyu da za a yi a birnin Geneva. Amma har ila yau kungiyar 'yan adawa ta kasar Sham ba ta yi alkawarin shiga taron ba tukuna.
Haddadiyar sanawar da aka bayar bayan taron ta yi kira da a kara baiwa 'yan adawa goyon bayan a fannin aikin soja, da siyasa, da kuma taimakawa musu wajen biyan bukatun jama'ar da ke shiyyoyin da suke mallaka, tare kuma da kafa gwamnatin wucin gadi cikin 'yan watanni masu zuwa, amma ba a gabatar da wa'adi na karshe ba cikin sanarwar.
Da tsokaci kan taron, shugaban zaman, kuma ministan harkokin wajen kasar Birtaniya William Hague, ya bayyana cewa, mahalarta taro sun kai ga cimma matsaya guda, musamman wajen karfafa hadin kai da sa kaimi ga aikin shimfida zaman lafiya a kasar Sham karkashin jagorancin MDD. Sa'an nan bangarori daban-daban sun yi kira ga sassan biyu da ke adawa da juna a kasar ta Sham da su shiga taro karo na biyu na kasa da kasa da za a yi a birnin Geneva a wata mai zuwa. (Amina)