Sashin kula da ayyukan kafofin yada labarai na BBCn ne ya dauki nauyin wannan bincike, wanda ya shafi mutane kimanin dubu 33, dake kasashen Asiya 7, da suka hada da Sin, da India, da Pakistan, da dai sauransu. Sakamakon binciken ya sheda cewa, bayan da aka yi musu tambayoyi, yawan jama'ar kasar Sin da suka fahimci ma'anar kalmar 'sauye-sauyen yanayi' ya kai kashi 86%, kana yawan mutanen da suka yarda da abkuwar sauye-sauyen yanayi ya kai kashi 78%, alkaluman da suka fi wadanda aka samu a sauran kasashe 6.
Har wa yau kuma, da yawa daga cikin jama'ar kasar Sin da suka amsa tambayoyin, sun bayyana amfani da kyakkyawan tsarin kafofin zirga-zirgar jama'a, da makamashi mai tsabta, a matsayin hanyoyin warware matsalar sauyin yanayi. Kana a ganin wadannan jama'ar kasar Sin, babbar manufar da kasarsu ta dauka don tinkarar matsalar ita ce, kyautata fasahar yin amfani da makamashi. (Bello Wang)