in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a girka cibiyar nazari kan canjin yanayi a kasar Kenya
2012-06-01 11:08:53 cri
Kasar Kenya za ta kasance da cibiya ta farko kan binciken kimiyya game da canjin yanayi. Wannan kuma zai taimaka wajen bunkasar kanfanonin da za su kawo anfani kan tattalin arziki daga abubuwan da muhalli ya kunsa a game da kokarin da kasashen duniya ke yi wajen rage samar da iska mai guba da ya kasance wani abun da ke dumama duniya baki daya.

Wannan sabuwar cibiya dai, wata kungiya mai sunan InfoDev ce za ta girkata, ita kuma kungiyar ta InfoDev ta kasance kungiya ce ta gungun masu jari a bankin duniya, wadda kuma tana da jarin da ya kai miliyon 6 na dalar Amurka.

Burin girka wannan cibiya shi ne, domin taimakawa kasashe masu tasowa wajen samun hanyar cin garabasar zuba jari domin rage gaugauwar canjin muhalli. Wannan abu kasance daya daga cikin manyan kangi da muhalin duniya ke fuskanta.

Valerie D'Costa, jami'i mai kula da tasre tsare na InfoDev, ya sanar da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin wato Xinhua a ranar Alhamis a Nairobi babban birnin kasar kenya cewa, burin wannan cibiya shi ne saukaka zuba jari ga kamfanonin da ke da halin bunkasa tattalin arziki ta bangaren gudanar da ayyuka ta fannin canjin muhalli. Da za su zuba jari ta fannin sabbi da tsoffin hanyoyin kasuwanci masu nagarta da ke da nasaba da fasalin zuba jari na yanzu da za a iya maye gurbinshi.

Wanna cibiyar da za ta kasance a Nairobi, za ta kuma kasance a inuwar wata hukuma ta kasar za ta jagorentar tafiyar da ayyukanta, sai dai daga nan zuwa watan Satumba na wannan shekara ne za a sani ko wace hukuma ce za ta jagoranci wannan cibiya domin tafiyar da lamuranta. Wannan cibiya ta kasance ta farko da aka fara kirkirowa a cikin kasashe daban daban masu tasowa na duniya. (Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China