in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kammala aikin tsara babban shirin tinkarar sauyin yanayin duniya
2011-12-07 21:08:36 cri
A ran Laraba 7 ga wata, Mr. Xie Zhenhua, mataimakin shugaban kwamitin ci gaba da yin gyare-gyaren kasar Sin ya bayyana a birnin Durban na kasar Afirka ta kudu, cewar kasar Sin za ta kammala aikin tsara babban shirin tinkarar sauyin yanayin duniyarmu nan gaba ba da dadewa ba.

A gun taron koli na tinkarar sauyin yanayin duniya da M.D.D. take shiryawa a Durban, Mr. Xie Zhenhua ya ce, a cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta gaggauta canja hanyar neman bunkasuwa a kokarin tinkarar sauyin yanayin duniya cikin hali mai yakini da kuma kara rage fitar da iska mai dumamar yanayin duniya. Ya ce, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tabbatar da jerin dokokin tinkarar sauyin yanayin duniya, alal misali, yawan iska mai dumamar yanayin duniya da za ta fitar zai ragu da kashi 17 cikin dari a shekarar 2015 bisa na shekara ta 2010. Bugu da kari, a cikin sabon babban shirin bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin, ta kafa burin da take son cimmawa kan yadda za ta kayyade jimillar makamashin da za ta yi amfani da shi a nan gaba.

Mr. Chris Huhne, minista mai kula da makamashi da batun sauyin yanayi na kasar Birtaniya, Mr. Corrado Clini, ministan kula da yankuna da muhalli da yankin teku na kasar Italiya, Mr John Leslie Prescott, tsohon mataimakin firaministan kasar Birtaniya dukkansu sun yaba wa burin rage fitar da iska mai dumama yanayi da kasar Sin take son cimmawa da sakamakon da ta riga ta samu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China