Xie Zhenhua ya yi wannan kalami ne a yayin bikin fara wani kwas da kasar Sin ta shirya wa kasashe masu tasowa domin tinkarar matsalar sauyin yanayi, kuma a cewarsa, kasar ta Sin za ta samar da taimako ga kasashe masu tasowa ta fannonin manyan ayyuka, fasahohin da za su yi tasiri kan matsalar sauyin yanayi, fasahohin yin tsimin makamashi da na sarrafa kayayyaki ta amfani da makamashin da za a iya sabuntawa, kana da inganta kwarewarsu.
Jami'ai sama da 60 da suka fito daga wasu kasashe sama da 30 da ke fuskantar koma bayan tattalin arziki, da wadanda ke kasancewa a kananan tsibirai da kuma nahiyar Afirka sun halarci kwas din.
A yayin da yake bayani kan taron da ake yi a Durban, Xie Zhenhua ya ce, Sin za ta ci gaba da taka rawar gani, kuma za ta kara daidaitawa da sauran kasashe, a kokarin neman cimma sakamako mai kyau a wajen taron.(Lubabatu)