in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen nahiyar Afrika dasu hada kansu game batun sauyin yanayi
2011-12-05 16:06:14 cri

A ranar hudu ga watan Disamba a birnin Durban na Afrika ta Kudu, wani kwararre kuma mai fafutuka a fannin kiyaye muhalli dan kasar Afrika ta Kudu ya bayyana cewa ya kamata gwamnatocin kasashen Afrika su dauki matakin kara tunaninsu kan batutuwan da suke da nasaba da sauyin yanayi tare da yin kira da a gabatar da wani tsarin aiki na hadin gwiwar kasashen nahiyar kan batun gurbacewar yanayi.

A cikin wata hirar da ya yi tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Asabar a yayin wani taron gangami na kishin kasa a albarkacin taro na 17 na bangarori daban daban kan kundin MDD bisa sauye sauyen yanayi (COP 17), Nkwame Cedile ya nuna cewa kungiyar cigaban tattalin kudancin Afrika SADC da tarayyar Afrika AU ya kamata su hada kai domin yin aiki tare ta yadda za'a cimma wata mafita ta Afrika cikin dogon lokaci game da matsalar sauyin yanayi.

"AU da SADC ya kamata su shirya taro da kuma daukar mataki guda da ya dace da halin da Afrika take ciki game da batun sauyin yanayi ba tare da bin wasu matakan manyan kasashen duniya da za su gaya masu ba", ya kara da cewa.

Dukkan muhimman kungiyoyin siyasa da hukumomin kudi na nahiyar Afrika, kamar bankin cigaban Afirka BAD, sun halarci wannan babban dandali na MDD na Durban domin tattaunawa kan sauyin yanayi.

"Ya kamata Afirka ta samu hanyar zuba kudi ta yadda za ta kasance cikin lokaci game da matsalar sauyin yanayi. Gwamnatocin kasashen Afrika ya kamata su sani cewa jiran kudade daga kasashen da suka cigaba zai dauki dogon lokaci" in ji mista Makhosonke Mdlalose wani fafufutukar kare muhalli.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China