Mr. Xie Zhenhua, mataimakin shugaban kwamitin neman ci gaba da yin gyare-gyare na kasar Sin ya yi wannan furuci a yau 21 ga wata a yayin wani bikin kammala taron bita karo na biyu kan nazarin batun sauyin yanayin duniya da na neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba da aka shirya a nan birnin Beijing.
Jami'ai 56 wadanda suka zo daga kasashe 20 na kananan tsibirai da kungiyar hada kan kasashen Afirka da wasu kasashe wadanda suke fama da kangin talauci suka halarci wannan taron bita da aka yi kwanaki 21 ana yinsa a nan kasar Sin.
Xie Zhenhua ya kara da cewa, a 'yan shekarun nan, kasar Sin ta kan sha hasarar rayukan jama'a da tattalin arziki sakamakon matsalolin sauyin yanayin duniya masu tsanani matuka. A lokacin da take fuskantar kalubaloli da nauyi a fannoni da yawa, kamar su raya tattalin arziki, kawar da talauci, kyautata zaman rayuwar jama'a da tinkarar sauyin yanayin duniya, kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa da kuma nuna wa sauran kasashe masu tasowa goyon baya wajen tinkarar sauyin yanayin duniya kamar yadda ta saba yi a da. Sannan ya jaddada cewa, dukkan kasashe masu tasowa suna da babbar moriya iri daya, don haka, kasar Sin tana son taiamakawa sauran kasashe masu tasowa bisa namijin kokarinta. (Sanusi Chen)