in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in kungiyar WTO ya yi kira ga bangarori daban-daban da su kiyaye tsarin yin ciniki tsakanin bangarori daban-daban cikin hadin gwiwa
2012-02-15 15:21:32 cri

Ranar Talata 14 ga wata a birnin Geneva, babban jami'in kungiyar cinikayya ta kasa da kasa (WTO) Pascal Lamy ya ba da rahoto a gun babban taron kungiyar, inda ya jaddada cewa, ya kamata bangarori daban-daban su dauki nauyin da ke kansu na sa kaimi ga shawarwarin Doha da kiyaye tsarin yin ciniki tsakanin bangarori daban-daban.

A cikin rahotonsa, Pascal Lamy ya bayyana shawarwarin da aka daddale a dandalin Dawos da taron koli na kungiyar tarrayar kasashen Afrika (AU). Ya ce, a halin yanzu, abin da za a yi wajen sa kaimi ga shawarwarin Doha shi ne tabbatar da ayyukan da suka samu amincewa daga bangarorin daban-daban, da kuma tattaunawa kan wasu matsalolin da ba a cimma matsaya a kansu ba.

Pascal Lamy ya ce, rukunonin yin shawarwari a karkashin jagorancin WTO na fara tattaunawa kan wannan batu.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China