Kakakin kungiyar ya yi kira ga taron Durban da ya kaddamar da asusun neman taimako game da batun yanayi na GCF domin ba da gudumuwa ga kasashe masu tasowa wajen samun kudin tinkarar batun sauyin yanayi.
Taron Cancun da aka yi a shekarar 2010 ya yanke shawara cewa, kasashe masu wadata su samar da kudi dala biliyan 100 a ko wace shekara daga shekarar 2013 zuwa 2020, amma duk da haka wannan ba zai biya bukatun wadannan kasashe ba.
Kungiyar AG na kunshe da kasashe 54, wadda ta zama muhimmiyar kungiya cikin shawarwarin sauyin yanayi. A ganin kungiyar, nahiyar Afrika ya fi fama da batun sauyin yanayi. Bisa kididdigar da wasu hukumomin MDD suka bayar, an ce, ya zuwa shekarar 2020, yawan mutanen nahiyar Afrika da za su yi fama da karancin ruwan sha zai kai miliyan 7.5 zuwa miliyan 25, kuma yawan hatsi da wasu kasashen Afrika za su samar zai ragu da kashi 50 bisa 100.(Amina)