in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron baje kolin fasahohin makamashi da canjin yanayi a Vienna
2012-11-20 11:07:44 cri

A ranar Litinin 19 ga wata ne dai aka bude taron baje kolin fasahohin makamashi da lura da sauyin yanayi, na kasashe masu tasowa na shekarar 2012 a Hofburg dake wajen birnin Vienna na kasar Austria. Taron baje kolin dai na burin gabatar da sababbin fasahohi da suka shafi makamashi da kuma kare muhalli ga barin gurbatarsa, sakamakon sauyin yanayi. Tuni dai hukumar MDD mai lura da cigaban masana'antu ta UNIDO, ta sanar da bude taron na bana, mai taken "Hadin kan kasashe masu tasowa a fannin makamashi da sauyin yanayi", kamar dai yadda babban daraktan hukumar ta UNIDO Kandeh K. Yumkella ya bayyana wa manema labaru ta wata sanarwar da aka raba. Haka zalika yayin da yake jawabin bude taron, Mr. Yumkella ya ce, gudummawar wadannan kasashe a fannin ci gaban duniya na da matukar tasiri, musamman idan aka lura da hasashen rawar da za su taka a fagen samar da ci gaba nan da shekarar 2030.

Cikin dai ababan da aka baje kolinsu yayin taron na wannan shekara, da zai gudana daga ranar 19 zuwa 23 ga wata, akwai fasahohin magance matsalolin da sauyin yanayi ka iya haifarwa, da ma hanyoyin warware matsalar makamashi dake addabar sassan duniya. Bugu da kari, kafin kammalar taro, ana sa ran masana za su tattauna kan irin ci gaba, da ma kalubalen da kasashe mahalarta taron ke fuskanta dangane da wannan al'amari, tare kuma da kokarin lalubo hanyoyin magance matsalolin dake tattare da hakan, baya ga batun samar da cigaban masana'antu, da lafiya, da ma samar da abinci.

A cewar mashiryansa, bikin na bana, zai ba da karin dama ta tattauna hanyoyin magance kalubalen da ke fuskantar nasarar cimma muradun karni na MDGs.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China