in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira ga kasashe masu wadata da su gabatar da shirin samar da kudaden tinkarar sauyin yanayi
2013-11-05 16:06:44 cri

Shugaban kungiya mai kula da harkokin sauyin yanayi ta kasar Sin, kuma mataimakin direktan kwamitin yin kwaskwarima, da raya kasar Sin Xie Zhenhua, ya bayyana a yau Talata 5 ga wata cewa, Sin na sa ran ganin kasashe masu wadata sun tantance kudin da za su samar, da zai isa bukatun da ake gudanarwa daga shekarar 2013 zuwa 2015,yayin taron tattaunawa kan sauyin yanayi da MDD za ta yi a birnin Warsaw na kasar Poland a wannan wata da muke ciki, tare kuma da fatan kasashe masu wadatar za su gabatar da shirin samar da kudi, da yawansa ya kai dala biliyan 100 nan da shekarar 2020.

Xie Zhenhua ya nuna cewa, Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa yayin taron, tare kuma da yin hadin gwiwa da ragowar kasashen duniya, domin goyawa mai masaukin taron wato kasar Poland baya, a kokarin cimma nasara da ake fata bisa ka'idar adalci, da shigo da bangarori daban-daban cikin taron, da tattaunawa a karkashin jagorancin masu ruwa da tsaki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China