in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Afrika ta Kudu ta yi kira da kara sabbin kokari domin yaki da sauyin yanayi
2012-05-06 16:30:56 cri
Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta yi kira a ranar Asabar ga gamayyar kasa da kasa na ta kara yawaita kokari wajen yaki da sauyin yanayi.

Dandalin MDD kan sauyin yanayi na shekarar 2011 ya taimaka ga kafa wani babban yunkuri na tunkarar kalubale kuma wannan yunkuri ya kamata a rike shi da kyau., in ji ministan harkokin waje da dangantaka na kasar Afrika ta Kudu Mista Maite Nkoana-Mashabane a cikin wata sanarwa.

Taron MDD kan sauyawar yanayi ya gudana a cikin watan Disamba da ya gabata a birnin Durban, kuma taron ya dauki wani rukunin matakai bisa batutuwan dake janyo hankali wanda a cikinsu akwai mataki na biyu na cika alkawuran yarjejeniyar Kyoto, gidauniyar kuka da yanayi da kuma sabon tsarin tafiyar da aikin da ya shafi aiwatar da alkawuran rage fitar da iska mai gurbata yanayi da muhalli bayan shekarar 2020, ministan ya kara tunatarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China