in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nelson Mandela na fama da rashin lafiya mai tsananin, in ji tsohuwar matarsa
2013-11-18 15:10:38 cri

Kafar yada labaru ta kasar Afrika ta kudu ta ba da labari a jiya Lahadi 17 ga wata cewa, Madam Winnie Madikizela-Mandela tsohuwar matar Nelson Mandela ta bayyana cewa, har yanzu Mandela na fama da rashin lafiya mai tsanani, wanda har ba ya iya mangana da bakinsa, sai dai ba'a saka shi ya dogara da na'urar jan rumfushi ba.

Yayin da ta zanta da wakilin jaridar Sunday Independent, Madam Winnie ta furta cewa, Nelson Mandela ba ya iya magana, saboda an sa wasu bututu cikin bakinsa, wadanda yake yin amfani da su domin tsamo ruwan da yake taruwa a cikin huhunsa ta yadda zai kaucewa sake samun ciwo a cikin huhu. Likitoci na fatan maido da karfin Nelson Mandela na yin magana, sai dai yanzu yana iya mu'amala da mutane ta hanyar alamar fuska kawai.

Nelson Mandela mai shekaru 95 a duniya ya dawo gidansa dake birnin Johannesburg a ran 1 ga watan Satumba bayan da ya shafe watanni uku yana kwance a asibiti, saboda fama da yake yi da ciwon huhu, an taba ba da labari cewa yana jiran lokaci ne kawai saboda yadda ciwon ya sha karfin sa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China