Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela wanda yanzu haka yake kwance asibiti yana jinya sama da watanni biyu yana murmurewa yadda ya kamata sai dai a hankali, in ji fadar shugaban kasar a ranar Lahadi.
Kakakin shugaban kasar Mac Maharaj wanda ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, ko da yake likitocin dake duba shi a asibitin sun tabbatar da samun saukin shi a hankali yadda ya kamata, duk da haka, sun ce, yana cikin wani yanayi mai tsanani.
Fadar shugaban kasar dai wadda ke da alhakin bayyana matsayin lafiyan Mandela ta dan yi shiru game da hakan fiye da kwanaki 10, duk da cewa yawan masu zuwa asibitin don mika fatansu na alheri sun dan ragu har ila yau Al'umma na ci gaba da nuna damuwarsu game da lafiyarsa.
Zindzi Mandela, diyar tsohon shugaban kasar a ranar Jumma'a ta ce, mahaifinta ya ji sauki sosai tun da yanzu haka yana iya zama a kan kujera na wassu dan lokaci, kamar yadda kafar watsa labarai ta kasar ta ba da rahoto.
Nelson Mandela mai shekaru 95 a duniya kuma tsohon dan gwagwarmaya da yaki da nuna wariyar launin fata, an kwantar da shi a asibiti ne tun ranar 8 ga watan Juni sakamakon ciwon huhu, abin da ya nuna a ranar Lahadin nan ya cika kwanaki 65 yana kwance a asibiti, wanda shi ne mafi tsayi a duk kwanciyar da ya sha yi tun daga watan Disamban bara. (Fatimah)