Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ya karyata jita-jitar da ake watsawa a ranar Alhamis dake bayyana cewa, Nelson Mandale na cikin wani yanayi na ruduwa.
Fadar shugaban kasar ta yi la'akarin da labaran da kafofin watsa labarai suke baiwa kan rashin lafiyar tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela, domin haka ne take son kawo karin haske, in ji wata sanarwa ta fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu. A ranar Alhamis, wasu kafofin kasar sun rawaito cewa, mista Mandela na cikin wani yanayi ruduwa na dogon lokaci kuma na'urori ne suke taimaka masa wajen yin numfashi. 'Muna tabbatar da sanarwar da muka bayar da yamma, bayan da shugaba Jacob Zuma ya kai wa Madiba wato Nelson Mandela ziyara a asibiti, hakika Mandela yana cikin yanayi mai wuya, amma yana samun sauki sannu a hankali.' in ji wannan sanarwa.
Likitoci sun karyata cewa, tsohon shugaban kasar na cikin wani yanayi na ruduwa, tare da jaddada cewa, Mandela na samun kulawa sosai daga wajen gungun kwararrun likitocin kasar.
Mandela mai shekaru 94, na samun jinya a asibitin Pretoria tun ranar 8 ga watan Yuni dalilin matsalar ciwon huhu. (Maman Ada)