in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jacob Zuma ya yi jawabin murnar cika shekaru 19 da kafuwar kasar Afirka ta kudu
2013-04-28 14:08:19 cri

Ranar 27 ga watan Afrilu na shekarar 1994 ne, aka fara yin amfani da tsarin mulkin na rashin nuna bambancin launin fata, haka kuma an mai da wannan rana a matsayin ranar kafuwar Afrika ta kudu. A ran 27 ga wannan wata bisa agogon wurin kuwa, wurare daban-daban na kasar sun yi murnar wannan rana. Shugaban kasar Jacob Zuma ya darajanta ci gaba da kasar ke samu bayan kafuwarta a birnin Pretori.

Ban da haka, Jacob Zuma ya tabo rikicin da ya auku a shekarar bara na harbe-harben da 'yan sanda suka kaiwa ma'aikatan da ke hakar ma'addinai a Marikana, ya ce, ko da yake a ganin wasu mutane, wannan batu ya kawo karshen kokarin da Afrika ta kudu ta yi na samar da dimokuradiyya, amma jama'ar kasar suna kishin kasarsu a matsayin farko, kuma sun yi hadin gwiwa wajen tinkarar wannan barazana tare da samun nasara. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China