Ministan ya fada wa manema labaru cewa, za a gabatar da labarunsu ta hanyar mujallu da jaridu da gidajen rediyo na kasar.
Haka kuma, an ce, wannan manufar da aka fitar na da ma'anar musamman, wajen ba da tabbaci wajen yaki da cin hanci da rashawa.
A cikin kwanaki masu zuwa, za a fidda da dukkan sunayen wadanda da aka tabbatar da laifin cin hanci da rashawa, kuma za a rufe asusun ajiyarsu, ko kuma a mayar da asusun ga gwamnati.
Haka kuma, ministan ya waiwayi baya game da kokarin da ya yi wajen yaki da cin hanci da rashawa, tun bayan da aka kafa sashen kula da yaki da cin hanci da rashawa a kasar a shekarar 2010.
Bisa kididdigar da Radebe ya bayar, an ce, an cafke mutane 237, tare da yin hukunci ga 32 daga cikinsu, haka kuma an wanke 2 daga cikin zargin da aka yi musu, sauran 203, sun fuskantar shari'a a halin da ake ciki.(Bako)