in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabbin ministocin kasar Afrika ta kudu sun yi rantsuwar kama aiki
2013-07-11 16:55:03 cri

Sabbin ministocin gwamnatin kasar Afrika ta kudu guda 9 sun yi rantsuwar kama aiki a yammacin ranar 10 ga wata a birnin Pretoria,hedkwatar kula da harkokin hukuma ta kasar.

Kafar yada labarai ta kasar ta ba da labari cewa, a cikin wadannan sabbin ministoci 9, ministan sadarwa Yunus ya taba zama mamban kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Afrika ta kudu, kuma ministar zaman rayuwar jama'ar kasar Connie Septempe ta kasance tsohuwar mataimakiyar shugabar kungiyar hadin gwiwar ma'aikatai ta kasar, wadda kuma ita ce 'yar majalisar dokokin jam'iyyar ANC ta Afrika ta kudu dake rike da shugabancin kasar.

A cikin wadannan sabbin ministoci, mambar kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ANC Pamela Tshwete ya zama mataimakin ministan hukumar raya kauyuka da harkokin filaye, wanda kuwa ya zama mamba daya tak a cikin sabbin ministoci da ya fito daga kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ANC.

A yammacin ranar 9 ga wata, shugaban kasar Jacob Zuma ya sanar da sauke ministoci 3 tare da nada sabbin ministoci da mataimakansu 9 bisa bukatar gaggauta kwaskwarima a kasar. Wannan ya kasance karo na hudu da Jacob Zuma ya yi garambawul ga majalisar ministoci bayan hawansa mukamin shugaban kasar a watan Mayu na shekarar 2009. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China