in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mandela na raye sosai, in ji jikansa
2013-09-02 14:41:52 cri

Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela na raye sosai, lamarin da ya sha bamban da rahotonnin da wasu kafofi suka bayar dake bayyana cewa, har yanzu ransa na ga hannun Allah, in ji jikan tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, mista Mandla Mandela a ranar Lahadi. Jikan na Mandela ya yi wannan furuci ne bayan da aka sallami Mandela daga asibiti bayan ya kwashe kusan watanni uku ana masa jinya game da cutar huhu da yake fama da ita. 'Dawo da mista Mandela gidansa na da muhimmancin gaske da ba da kwarin gwiwa domin kawar da karya da jita jitar da wasu suke yadawa na cewa, har yanzu ransa na ga hannun Allah ana jira ne kawai a janye na'urorin dake taimaka masa yin numfashi.' in ji mista Mandla a cikin wata sanarwa. Haka kuma ya bayyana cewa, fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu ta yi aiki sosai wajen sanar da al'ummar kasa game da halin rashin lafiyar Mandela maimakon yada rahotonnin karya na halin da tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu yake ciki da wasu mutane suke yadawa. A cewar fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu, ya koma gidansa dake birnin Johannesburg a ranar Lahadi da cewa, yana fama da rashin lafiya, haka kuma an gyara gidansa da na'urorin likita, ta yadda za'a cigaba da ba shi jinya yadda ya kamata, in ji fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China