Jiya Talata 7 ga wata, shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya yi kira da a kafa wata rundunar ko ta kwana karkashin AU, ta yadda za ta yi shiga tsakani idan wani rikici ya faru a nahiyar Afrika.
Shugaba Zuma bayan shawarwarin da ya yi da Shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan wanda ke ziyara a kasar ta Afrika ta kudu, ya yi bayani ga manema labarai cewa, wannan runduna idan aka kafa ta za ta kara karfin AU, da kuma taimaka wajen tabbatar zaman lafiya da karko a yankin. Yana mai nuni da cewa, ganin irin rikice-rikice da ya faru a Mali, jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Kongo Kinshasa, akwai bukatar a kafa irin wannan runduna cikin gaggawa.
Goodluck Jonathan dai ya isa kasar Afrika ta kudu a ran Talata 7 ga wata, wanda daga bisani zai halarci taro na yankin Afrika na dandalin tattalin arziki na kasa da kasa da za'a bude a yau Laraba 8 ga wata a birnin Capetown. (Amina)