in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu fatan alheri suna cigaba da yiwa Mandela addu'a a Afrika ta Kudu
2013-07-01 10:17:47 cri

A Pretoria, fadar gwamnatin kasar Afrika ta Kudu. al'ummomi daga sassa daban daban na duniya sai ci gaba suke da yin tururuwa a harabar asibitin da tsohon shugaban kasar Nelson Mandela ke kwance, suna mashi addu'an samun sauki cikin gaggawa.

Mandela dai yana kwance ne a asibitin tun ranar 8 ga watan jiya na Yuni, inda ake masa magani game da cutar huhu da yake ta fama da shi.

A ranar Asabar, shugaba Jacob Zuma ya shaida ma shugaban Amurka Barrack Obama dake ziyara a kasar cewa, yanayin lafiyar da Mandela ke ciki na kara tabarbarewa, amma yana fatan zai samu sauki ya kuma koma gida cikin lokaci.

A jiya Lahadi, al'ummomi da dama sun mamaye gaban asibitin suna addu'o'i da wake-wake na fatan Mandela zai samu sauki. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China