Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta sanar da cewar, tana nan tana gina wani mutum mutumi mai tsayin mitoci 9 da za'a shafe shi da ruwan tagulla na tsohon shugabanta Nelson Mandela domin kafawa a fadar shugaba kasar dake birnin Pretoria a watan Disamba mai zuwa.
Ministan fasahohi da al'adun kasar Paul Mashatile wanda yake jawabi ga manema labarai a cibiyar tunawa da Mandela dake birnin Johannesburg ya yi bayanin cewa, mutum mutumin wani hanyar cigaba ne da tunawa da gwagwarmayar da Mandela ya yi na yaki da wariyar launin fata da kuma samar wa kasar 'yancin kai da walwala cikin adalci.
Kafa wannan mutum mutumin a fadar shugaban kasar yana cikin wani kokarin da gwamnatin kasar ke yi na tattara duk alamun da za su sa a waiwayi baya domin nuna kudurin da al'ummar ke da shi a matsayinsu na 'yan kasar da ganin an daukaka darajarta, in ji Mr. Mashatile.
Shi dai wannan mutum mutumin, ana sa ran shugaba Jacob Zuma ne zai kaddamar da shi a ranar 16 ga watan Disamba.
Fadar shugaban kasar a shekarun baya ta kasance na farar fata ne da suka yi musu mulkin mallaka da daniya, har sai a shekara ta 1994 da kasar ta samu 'yan cin kanta.
Mutum mutumin, sanannun malaman zane-zane na kasar Andre Prinsloo da Ruhan Van Vuuren ne ke aikin gina shi. (Fatimah)