in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu ta shirya yin bikin shekaru 95 da haihuwar Mandela
2013-07-02 10:03:35 cri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya ce, al'ummar kasar sun yi shirin yin bikin cika shekaru 95 na haihuwar jagoran yaki da wariyar launin fata kuma tsohon shugaban kasar Nelson Mandela wanda yanzu haka yake kwance a asibiti a Pretoria kusan makonni uku sakamakom ciwon huhu da ya ki ci ya ki cinyewa.

Shugaba Zuma wanda ya fadi hakan bayan ziyarar Mandelan a asibitin ya ce, Mandela har yanzu yana cikin mawuyacin hali, amma yana samun sauki a hankali, don haka yake tuni ga daukacin al'ummar kasar da su fara shirye-shirye na yin bikin cika shekaru 95 na Mandela a ranar 18 ga wannan watan.Yana mai bayanin cewa, ya kamata a yi wani abin kirki ma al'umma a wannan rana, a kuma tuna da gwagwarmayan da tsohon shugaban kasar ya yi, yana mai godiya ga dukkan jama'an kasar da suka ci gaba da yin addu'o'i ga Mandelan da kuma iyalansa.

A cewar shugaba Zuma, suna fatan nan ba da dadewa ba Mandela zai ji sauki har a sallame shi ya koma gida, wannan furuci ya ba da wani kwarin gwiwwa ga al'ummar kasar.

Ya zuwa yanzu dai, wannan ne sanarwar ta baya baya da gwamnatin kasar ta fitar.

Haka shi ma kakakin majalissar dokokin kasar Max Sisulu bayan da ya ziyarci Mandelan a asibiti ya ce, tabbas yana samun sauki, abin da ya sa su jin dadin wannan sakamako.

Ranar haihuwar Mandela 18 ga watan Yuli dai, MDD ta tsai da shi a matsayin ranar Mandela a shekara ta 2009, kuma wannan ne karo na hudu da za'a yi bikin wannan rana, inda kungiyoyi daban daban suka gama tsara ayyukan da za su gabatar domin bikin wannan ranar wadanda suka hada da kade-kade da taron al'umma, da ma ayyukan ba da tallafi ga marasa galihu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China