Hukumar kiwon lafiya ta kasar Afrika ta kudu ta sanar da wani sabon magani na yaki da cutar Sida a jiya Litinin 8 ga wata a Pretoria, babban birnin kasar, wanda zai iya rage yawan magungunan da wadanda suka kamu da ciwon AIDS suke sha, sannan ya rage yawan kudin da suke kashewa, tare kuma da kara taimaka masu samun sauki.
Hukumar watsa labaru na kasar Afrika ta kudu SABC ya ba da labari cewa, gwamnatin kasar za ta samar da irin maganin ga mutane dubu 180 da suka hada da mata masu juna biyu, da matan dake shayarwa, da kuma sabbin mutanen dake dauke da cutar ta AIDS. (Bilkisu)