Ran 2 ga wata, yayin ganawarsa tare da wakilan ketare a taron majalisar zartaswa da aka yi a nan birnin Beijing, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, za a fitar da shirye-shiryen yin gyare-gyare na kasa daga dukkan fannoni yayin cikakken zama karo na uku na kwamitin tsakiya na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.
Ran 1 ga wata da dare, firaminista Li Keqiang ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta zurfafa ayyukanta wajen yin gyare-gyare kan fannonin haraji, sha'anin kudi, kamfanoni da dai sauransu.
Kan lamarin, wata jaridar kasar Spain ta bayyana cewa, kasar Sin ta mai da hankali sosai kan ayyukan kyautata zaman rayuwar al'umma da kuma yin kwaskwarima da kasar Sin ke aiwatarwa, wanda babu shakka zai taimaka mata wajen samun matukar bunkasuwa a nan gaba.
Bugu da kari, ran 6 ga wata, jaridar Financial Times ta Burtaniya ta rubuta wani sharhi cewa, matakan da shugabannin kasar Sin suka dauka sun gyara bambancin ra'ayoyin da wasu al'ummomin kasa da kasa suka nuna game da kasar kan fannonin tattalin arziki da tsarinta na siyasa. (Maryam)