in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasa da kasa suna maida hankali kan cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18
2013-11-08 17:01:42 cri

Kafin gudanar da cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na karo na 18, masana na kasashen waje sun yi tsammani cewa, gudanar da wannan taro a wani lokaci mai muhimmanci da ake yin kwaskwarima a kasar Sin yana da babbar ma'ana, wanda zai tsara sabuwar hanyar da za a bi wajen raya kasar a nan gaba.

Tsohon sakataren kudi na kasar Amurka Henry Paulson ya bayyana cewa, sabon kudurin da za a tsara a gun cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18 zai nuna hanyar da kasar Sin za ta bi wajen samun bunkasuwa mai dorewa. Yana sa ran cewa, gyaran da za a yi wa tsarin tattalin arzikin kasar Sin zai shafi harkokin kasuwancin kasar, kara bada dama ga kamfanonin kanana da matsakaici, kara yin amfani da kudi, kyautata dangantakar dake tsakanin kashe kudi da zuba jari da dai sauransu.

Wani mai nazari kan harkokin kasar Sin a kasar Faransa Leonel Veron ya nuna cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu a shekaru fiye da 30 da suka wuce ya kyautata rayuwar yawancin Sinawa. A halin yanzu, burin jama'ar Sin ya canja, sun kara bukatar yaki da cin hanci da yin kwaskwarima mai zurfi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China