in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18 a birnin Beijing
2013-11-09 17:36:29 cri
Tun daga ranar 9 zuwa 12 ga wata, za a gudanar da cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, inda za a yi nazari kan yadda za a zurfafa ayyukan kwaskwarima daga dukkan fannoni a kasar. Wanda hakan ke nuna mana cewa, a halin yauzu, an riga an shiga wani sabon matsayi tun lokacin Sin ta fara bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978.

Shugabannin kasar Sin sun bayyana cewa, gyare-gyaren da za a yi a nan gaba za su shafi fannoni daban daban, kuma babu shakka za su iya ciyar da harkokin raya tattalin arzikin kasar gaba.

Shehu malami na makarantar jam'iyya ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin Wang Huaichao ya bayyana cewa, yin kwaskwarima a kasa na da muhimmiyar ma'ana ga bunkasuwar kasar Sin. Kana, shi ma wani shehu malami Mr.Qin Gang ya nuna cewa, abin da ya fi muhimmanci cikin harkokin yin kwaskwarima shi ne, a amsa fata da kuma bukatun jama'ar kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China