Za a gudanar da cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, kafofin watsa labaru na kasa da kasa na cewa, a yayin taron ne za a tsara makomar bunkasuwar kasar Sin da manufofin yin kwaskwarima a shekaru 10 masu zuwa, wanda zai bada taimaka da bada kwarin gwiwa wajen farfado da tattalin arzikin duniya, da kuma nemawa kasar hanyar neman ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma.
Jaridar WallStreet ta kasar Amurka ta bayar da wani labari a shafinta na internet, inda ta ce, dukkan duniya za ta maida hankali kan gabatar da manufofin yin kwaskwarima na kasar Sin. Kana kamfanin dillancin labaru na Reuters ya maida wannan batu na labarin tattalin arziki a matsayin mafi muhimmanci a wannan lokaci.
Yayin da ake fuskantar matsalolin tattalin arziki a duniya, kasashen Turai da kasar Amurka suna fatan kasar Sin za ta taimaka wajen farfado da tattalin arzikin duniya. Babu shakka, yin kwaskwarima a kasar Sin zai kawo kyakkyawar makoma da imani ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.
Ban da wannan kuma, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun yi ganin cewa, yin kwaskwarima a kasar Sin zai nuna hanya ga sauran kasashen duniya a wannan fanni. Jaridar The British "Financial Times" ta bayar da wani sharhi cewa, watakila manufofin Sin na yin kwaskwarimar tattalin arziki za su bada misali ga sauran kasashen duniya a wannan fanni. Wasu masana na Afirka da Asiya suna ganin cewa, Sin ta dauki matakan da suka dace wajen yin kwaskwarima, neman samun bunkasuwa da karko, wadanda suka bada fasahohi ga sauran kasashen duniya. (Zainab)