Rahoton da aka gabatar bayan cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18 ya nuna cewa, yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki zai zama wani muhimmin fanni ga kasar Sin wajen zurfafa gyare-gyare a dukkan fannoni, batun da ke ginshikin gyare-gyare wajen daidaita dangantakar da ke tsakanin gwamnati da kasuwanni, don kasuwanni su taka rawa mafi muhimmanci yayin rarraba albarkatun kasa tare da nuna amfanin gwamnati yadda ya kamata.(Danladi)