Kafofin watsa labaran ketare suna mai da hankali kan cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18
Yayin da aka bude cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na karo na 18, kafofin watsa labaran ketare suna ganin cewa, ana gudanar da wannan taro na wannan lokaci yayin da harkokin kwaskwarinar kasar ta Sin suka shiga wani muhimmin lokaci, kuma babu shakka za a fitar da manyan manufofi dangane da zurfafa ayyukan kwaskwarima daga dukkan fannoni da kuma inganta ayyukan bunkasuwar tattalin arziki.
Bisa labarin da jaridar Financial Times ta Burtaniya ta bayar, an ce, a nan gaba, kasar Sin za ta mai da hankali kan harkokin samun dauwamammen ci gaban tattalin arziki.
Haka zalika, kamfanin dillacin labaran kasar Faransa ya bayyana cewa, Sin za ta samar da manufofin bunkasa da yin gyare-gyare ga fannin tattalin arziki a yayin cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18. (Maryam)