A cewar shugaba Xi, har yanzu kasar Sin na fuskantar kalubaloli da yawa a kokarinta na neman ci gaba, sa'an nan kuma samun ci gaban tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a, sun ci gaba da zama aikin farko ga gwamnatin kasar.
Haka zalika, shugaba Xi Jinping ya yi tsokaci kan yanayin da tattalin arzikin Sin ke ciki, inda ya ce a halin yanzu tattalin arzikin kasar na cikin wani nagartaccen yanayi, yana kuma samun ci gaba, don haka shi da sauran shugabannin kasar suna da imani sosai, na cewar tattalin arzikin kasar zai haifar da wani yanayi na ci gaba yadda ya kamata.
A daya bangaren kuma, shugaba Xi ya nanata cewa, kasar Sin za ta kara daukan nauyin lura da lamuran kasa da kasa, da kokarin taka rawa a kwaskwarimar da ake wa tsarin duniya da na harkokin kasa da kasa, bisa ci gaban da kasar ta samu a fannin tattalin arziki, ta yadda za a iya tabbatar da ganin ci gaban kasar, ya haifar mata da karin jituwa da sauran kasashen duniya. (Bello Wang)