in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta gabatar da ajanda da taswirar kwaskwarima da za ta aiwatar
2013-11-01 16:07:29 cri

Za a kira cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwamins ta Sin a karo na 18 a nan gaba kadan, a ran 31 ga watan Oktoba, kungiyar kwararru ta Brookings ta kasar Amurka ta kira taron kara wa juna ilmi a birnin Washington, inda ake nuna hangen hasken gobe ga cikakken zaman din da Sin za ta yi daga ran 9 zuwa 12 ga wata a nan birnin Beijing. Masani mai kula da harkokin kasar Sin na kungiyar Mr Li Cheng ya yi hasashen cewa, shugabannin kasar Sin za su gabatar da shirin kwaskwarima kan wasu manyan fannoni ciki hadda hada-hadar kudi, raya birane, filaye da sauransu.

Li Cheng ya babbaya cewa, yana sa ran samun nasara ga kwaskwarimar da kasar Sin ke yi daga yawancin fannoni, saboda dukkansu sun shafi batutuwa masu muhimmanci a nan kasar Sin yanzu, yana fatan taron zai sa kaimi ga kyautata tattalin arzikin kasar Sin, musamman ma hadar hadar kudi. A sa'i daya kuma, Li Cheng yana ganin cewa, cikakken zaman zai gabatar da ajanda da taswirar kwaskwarimar da gwamnatin kasar za ta aiwatar nan gaba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China