Ofishin kula da harkokin mataimakin shugaban kasar Amurka ya ba da wata sanarwa a jiya Litinin 4 ga wata cewa, mataimakin shugaban kasar Joseph Biden zai kawo wa kasar Sin ziyarar aiki a farkon watan Disamba mai zuwa, abin da ya kasance karo na biyu da zai ziyarci kasar Sin bayan shekarar 2011.
Sanarwar ta bayyana cewa, a lokacin ziyararsa a nan birnin Beijing, Biden zai gana da shugabannin kasar Sin domin tattauna wasu manyan batutuwa dake shafi shiyya-shiyya da ma duniya wadanda suke jawo hankalin kasashen biyu. (Amina)