in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin tunawa da mamayar da Japan ta yi wa kasar Sin a wurare da dama na kasar Sin
2013-09-19 14:43:21 cri

Ranar 18 ga wannan wata rana ce ta cika shekaru 82 da kasar Japan ta kai hari a nan kasar Sin wanda a ke kira harin ranar 18 ga watan Satumba, wurare da dama sun yi bikin tunawa da wannan rana, ciki hadda birnin Shenyang, Xi'an, Beijing, Nanjing da sauransu.

A wannan rana da karfe 9 da mintoci 18 na safe, an kada jiniya a dakin ajiye kayayyakin gargajiya na tunawa da harin ranar 18 ga watan Satumba dake birnin Shenyang. Ban da haka, da karfe 9 da mintoci 16 na safe, mutanen da suka taru a fili sun kada kararrawa har sau 14 wanda ke nufin cewa, Sinawa sun kwashe shekaru 14 suna yakin kin harin Japanawa.

A wannan shekara da muke ciki ta bambanta da sauran shekaru, saboda kasar Japan ta rika tada rigingimu kan batun tsibirin Diaoyu, abin da ya fusata Sinawa sosai, hakan ya sa, jiniya da aka kada a wannan rana ta bayyana bakin cikin Sinawa matuka a cikin shekaru 82 da suka gabata.

A nan birnin Beijing, mutane da dama sun taru a dakin tunawa da yakin kin Japan, ban da haka, karo na farko ne dakin ya gabatar da wasu takardun shaida da suka bayyana laifufukan da Japan ta aikata na garkuwa da gwarzayen Sinawa zuwa kasar Japan.

A birnin Nanjing kuwa, dakin ajiye kayan gargajiya na gidan kurkukun Auschwitz na kasar Poland, dakin tunawa da yakin kin harin Japanawa, dakin tunawa da 'yan gudun hijiran Yahudawa dake birnin Shanghai da kuma dakin tunawa da kisan gillar da Japan ta yi a birnin Nanjing sun hada kai wajen gabatar da hotuna dake bayyana laifin da aka aikata a gidan kurkuku na Auschwitz. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China