Wang Yi ya bayyana cewa, a halin yanzu abin da ya fi dacewa a baiwa muhimmanci tsakanin bangarori daban daban na kasar ta Syria shi ne, hada kai da nuna goyon baya ga kokarin da wakilin musamman na MDD, da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa game da warware matsalar Syria ya gabatar, tare da shiga taron Geneva ba tare da gindaya wani sharadi ba.
Ban da wannan kuma, kasar Sin na fatan kasashen dake yankin, za su cimma ra'ayi daya wajen ba da taimako, a matsayinsu na musamman don yin kira da a gudanar da taron Geneva ba tare da bata wani lokaci ba, da kuma aiwatar da sanarwar Geneva daga dukkan fannoni.
Ya kuma kara da cewa, ya kamata gamayyar kasashen duniya su samar da dama mai kyau, wajen gudanar da taron Geneva karo na biyu, bai kuma dace kasashen waje su sanyawa kasar Syria shirin warware matsala na siyasa ba.
Bugu da kari, Wang Yi ya ce yanzu masanan Sin sun riga sun karbi gayyatar da aka yiwa musu, don shiga ayyukan kawar da yaduwar makamai masu guba a Syria, ya ce idan akwai bukata Sin za ta samar da taimakon kudi. (Maryam)